DJ Ab - Yar Boko

This is Thug Life Mixtape
My African Sisters Star
Ok Let's go
Its a killer by DJ A.B

Wai bata cin tuwo kuma bata shan koko
Wai saidai coke ita bata shan zobo
Ita bata hawa machine wai sai dai motor
Ni na shiga uku na dauko 'Yar boko
In kaji ta kiraka she want spend your money
In Kaji tana ta karyar turanci she want spend your money
To gani nan dai na faka, she want chop my money
Eh nina shiga uku na dauko 'Yar Boko

Da 200 box natashi ina manage
Naje wurin mai suya ya yanka min da cabage
Na loda katin 100 na kira Hommie na Bebeji
Ina ta faman magana shiru ashe ma bai ji!..
Network was poor as the rain was falling
Babu wurin chilling ko ina naje boring
Sai BB na ta ringing ashe yarinya ke calling
Ina amsawa sai tace min darling
I need help pls A.B I need you
Come pick me up
Come with car and don't forget to come with your ATM card
Maganar ta da dadi muryarta kaman Waka
Ta zuba min british english duk nabi na rude
Na nemo key dakin baba na nan take na bude
Na debi wasu kudi 'kar'kashin pillow na ware
Jikina sai rawa ya ke har na manta ma in kulle..

Wai bata cin tuwo kuma bata shan koko
Wai saidai coke ita bata shan zobo
Ita bata hawa machine wai sai dai motor
Ni na shiga uku na dauko 'Yar boko
In kaji ta kiraka she want spend your money
In Kaji tana ta karyar turanci she want spend your money
To gani nan dai na faka, she want chop my money
Eh nina shiga uku na dauko 'Yar Boko

Na manna mota a guje bani niyyar in tsaya
Gashi motar dana dauka ba mai ta kusa ta tsaya
Saina ga dan bunburutu by my right saina tsaya
Na bude mashi tanki saiya kara gallon daya
Bayan na saka mai saina kama hanya
Ban ma san inda zani ba saina buga mata waya
Wai ashe ma tana gida sai nace gani nan zuwa
Harda cewa inyi sauri wai dan tana jin yunwa
Gidansu ba'a tuwo, Gidansu Ba'a koko
Bata san menene 'kuli ba balle ma ince rogo
Gashi ita bata girki abinci saidai a siyo
Driver'n su yayi tafiya sai gani nan na iso
Daga gani na kawai ta daka wani tsalle
Ta rungumeni da karfi saura kadan ma in balle
Yarinyar nan fresh fuskarta babu bulle
Gashi tashi kwalliya malam jikintaa harda lalle

Wai bata cin tuwo kuma bata shan koko
Wai saidai coke ita bata shan zobo
Ita bata hawa machine wai sai dai motor
Ni na shiga uku na dauko 'Yar boko
In kaji ta kiraka she want spend your money
In Kaji tana ta karyar turanci she want spend your money
To gani nan dai na faka, she want chop my money
Eh nina shiga uku na dauko 'Yar Boko

Na kaita shopping mall ta maida ni dan dako
Don ni kaina bana iya kirga kayan dana dauko
Yarinya 'Yar boko ta maidani kamar Tom
Yan mata 'Yan boko kuji tsoronsu kamar Bomb
Mun fito shiga mota wai ita zata tuka
I know you are tied baby koma can ka huta
Tai mun dadin baki ni kuma soko sai na bata
A tashin farko tai sama da yellow fever
Saboda haka police sukaa kaini station
Suka kira babana sukace yaronka na station
Ashe shima nema na yake sai gasu a station
The girl disappered from the massive situation
Da babana ya shigo banji ta da dadi ba
Nasha duka nasha wahala ban cikin haiyacina
Wai sai nayi 2 weeks sannan za'ai bailing dina
In kuma na fito wai za'a kaini Rehab house

Wai bata cin tuwo kuma bata shan koko
Wai saidai coke ita bata shan zobo
Ita bata hawa machine wai sai dai motor
Ni na shiga uku na dauko 'Yar boko
In kaji ta kiraka she want spend your money
In Kaji tana ta karyar turanci she want spend your money
To gani nan dai na faka, she want chop my money
Eh nina shiga uku na dauko 'Yar Boko